ABNA24 : Hakan a cewarsa domin mika ragamar kasar ga wanda aka amincewa tafiyar da gwamnatin yayin tattaunawar dake gudana ta tsakanin ‘yan kasar domin kawo karshen rikice rikicen da kasar ke fama da shi.
Shugaban gwamnatin ta Tripoli dake samun goyan bayan MDD, ya bayyana hakan ne a cikin gajeren jawabin da ya gabatar da yammacin jiya.
A tsakanin ranakun 6 zuwa 10 ga watan Satumban nan ne bangarorin dake rikici da juna a kasar ta Libiya, suka koma kan teburin tattaunawa wacce ba ta kai tsaye ba, a biranen Montreux na Swizilland, da kuma Bouznika a Morocco, da nufin lalubo hanyoyin magance rikicin da ya dabaibaye kasar.
Tattaunawar dai na maida hankali ne kan yadda za’a kafa majalisar shugabanci da kuma nada sabon shugaban gwamnati wanda zai karbi aiki cikin ruwan sanyi, wanda ta hakan ne za’a shirya zabuka.
Libiya dai ta fada cikin rudani ne tun bayan kifar da mulkin tsohon shugaban kasar mirigayi Mu’ammar Ghaddafi a cikin shekara 2011, inda yanzu haka kasar ke fama da gwamnatoci guda biyu, ta Fayez Al-sarraj a Tripoli dake samun goyan MDD, sai kuma ta Khalifa Haftar dake rike da ikon gabashin kasar.
342/